• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAWURI-AN CETO MALAMAI BIYU DA DALIBAI BIYAR

Sojoji sun baiyana ceto malamai biyu da dalibai biyar na makarantar sakandaren gwamnati ta Yawuri da masu satar mutane su ka sace su.

Sojojin a karakshin runduna mai  taken “hadarin daji” sun baiyana fafatawa da barayin inda har ma su ka kwato shanu 800.

Rahoton daga sabon kakakin soja Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya baiyana cewa barayin sun kasu gida biyu tsakanin wadanda ke dauke da daliban da wadanda ke kora shanun sata.

Sojojin ta taimakon sojan sama sun yi musayar wuta inda cikin juyayi daya daga daliban mata ta riga mu gidam gaskiya saboda galabaita.

Za a mika daliban biyar da malaman biyu hannun gwamnatin jihar Kebbi yayin da a ke yunkurin ceto sauran daliban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *