• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAWAN MUTANE DA SUKA RASA RANSU A HARIN GIWA SUN KAI MUTUM 38

ByNoblen

Dec 20, 2021 , , ,

Zuwa yanzu yawan mutanen da su ka rasa ran su a harin da ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa a jihar Kadunada sun kai mutum 38.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya baiyana cewa an gano sunayen mutum 29 cikin wadanda a ka yi wa kisan gillar yayin da sauran ba a gano sunayen su ba.
Tuni ma gwamnatin jihar ta wallafa sunayen marigayan.
Kazalika maharani sun kona gidaje da motoci da sauran dukiyoyin jama’a.
Gwamnan jihar Kaduna ya jajantawa al’ummar yankin bisa aukuwar wannan akasin da kuma umurtar hukumar agajin gaggawa ta duba lamarin don kai kayan tallafi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YAWAN MUTANE DA SUKA RASA RANSU A HARIN GIWA SUN KAI MUTUM 38”
  1. I have read several excellent stuff here. Definitely value
    bookmarking for revisiting. I surprise how a lot effort you place to make this type of wonderful informative web site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.