• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAU SHUGABAN AMURKA NA 46 JOE BIDEN KE SHAN RANTSUWA

A yau Larabar nan shugaban Amurka na 46 Joe Biden zai sha rantsuwar karbar ragamar mulki.

Za a gudanar da taron rantsuwar a “CAPITOL” da ke birnin Wahington DC bisa jagorancin babban alkalin Amurka John G. Roberts.

Bayan rantsuwar da ba za ta samu halartar dandazon jama’a ba don hana yaduwar cutar korona, Biden zai yi jawabi da kuma tafiya fadar WHITE HOUSE don fara mulkin shekaru hudu nan gaba na inuwar jam’iyyar sa ta dimokrats.

Biden ya zama shugaban Amurka mafi tsufa a lokacin karbar mulki a tsakanin dukkan wadanda su ka hau karagar 45 a baya.

A nuwamba mai zuwa Biden zai cika shekaru 78.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.