• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAU A KE CIKA SHEKARU 20 DA HARI KAN CIBIYAR KASUWANCI TA DUNIYA A AMURKA

Yau asabar din nan a ke cika shekaru 20 da kai hari cibiyar kasuwanci ta duniya a Amurka.

Harin dai an kai shi ne da amfani da jirgin sama da ya zama abun mamaki don an jingine makamai an yi amfani da jirgin fasinja wajen aukawa dogon benen a birnin New York.

Fiye da mutum 3000 su ka rasa ran su a sanadiyyar harin.

Tsohon shugaban Amurka George Bush Junior ya kaddamar da yaki da ya zaiyana da na ta’addanci a lokacin.

Yakin da ya biyo bayan harin ya shafi rayukan dubban mutane ciki kuma har da kai wa ga sanadiyyar kisan gilla ga wasu manyan jagororin kasashe da su ka hada da shugaban Libya Kanar Moammar Ghaddafi inda kuma Amurka ta jagoranci hari kan Iraki har a ka kawar da gwamnatin marigayi Saddam Huseeini.

Masu sharhi na ganin neman bude sabon babi ne ya sanya Amurka janyewa daga Afghanistan da ita ma Amurka ta mamaye shekaru 20 da su ka wuce.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *