• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YARJEJENIYAR “IBRAHIMIYYA” BA TA SAUYA RAYUWAR PALASDINAWA BA-JAKADAN TARAIYAR TURAI

ByMardiya Musa Ahmed

Aug 24, 2022

Jakadan taraiyar turai a gabar ta tsakiya Seven Koopmans ya baiyana cewa yarjejeniyar da Isra’ila ta cimma ta huldar arziki da wasu kasashen larabawa mai taken “IBRAHIMIYYA” ko “ABRAHAM ACCORD” a turance ba ta sauya rayuwar Palasdinawa ba.

An cimma wannan yarjejeniya da jagorancin tsohon shugaban Amurka Donald Trump inda tsohon firaministan Isra’ila ya rantaba hannu kan dawo da dangantaka da wasu kasashen larabawa don alakar tarihi da ta samo tushe daga Annabi Ibrahim alaihis salam.

Jakada Koopmans ya ce abun da ya fito fili shi ne samun sauyi mai yiwuwa ne don alakar da a ka gani tsakanin kasashen, amma hakan bai sauya komai a rayuwar Palasdinawa ba.

Amurka karkashin gwamnatin Joe Biden ma ba ta sauya manufar Amurka ta mara baya ga samun kafuwar kasar Palasdinawa mai ‘yanci gefe da kasar Isra’ila ba.

Tun cimma yarjejeniyar da manyan kasashen larabawa irin su Daular Larabawa, shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya yi Allah wadai da shirin da zargin ‘yan uwan su larabawa da cin amanar su.

Shugaban Turkiyya Rcaeb Tayyib Etrdoan ma ya caccaki kasashen larabawan da su ka shiga yarjejeniyar da nuna hakan tamkar watsi da hakkin ‘yan uwan su Palasdinawa ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.