• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YARIMAN BAKURA YA AIYANA ZAI NEMI TIKITIN TAKARAR SHUGABAN KASAR NAJERIYA A INUWAR APC

Tsohon gwamnan Zamafara Sanata Sani Yariman Bakura ya aiyana niyyar neman tikitin takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar APC a 2023.

Bakura wanda ya shaidawa manema labaru wannan aniya a Abuja, ya ce ya na son takarar don kawo gyara kan lamuran tsaron Najeriya da su ka tabarbare.

A 2007 Yariman Bakura ya taba neman tikitin a inuwar ANPP amma sai shugaba Buhari ya samu nasarar samun tikitin.

Alamu na nuna APC ka iya samun turjiyar neman takara daga yankin kudu maso yamma na Yarbawa bayan kammala wa’adi biyu na shugaba Buhari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YARIMAN BAKURA YA AIYANA ZAI NEMI TIKITIN TAKARAR SHUGABAN KASAR NAJERIYA A INUWAR APC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.