• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YARIMA MUHAMMAD BIN SALMAN YA GANA DA SHUGABA ERDOAN A ANKARA

ByYusuf Yau

Jun 23, 2022

Yarima Muhammad bin Salman ya kammala rangadin kasashe uku da ya yi da ganawa da shugaba Raceb Tayyib Erdoan na Turkiyya.

Tun farko Muhammad bin Salman ya ziyarci Masar da Jodan inda ya gana da shugaba Abdelfatah Elsisi da kuma Sarki Abdullah bin Hussain.

Shugaba Erdoan ya karrama Yarima Muhammad a fadar gwamnatin Turkiyya a birnin Ankara.

Shugabannin biyu sun tattauna kan lamuran da su ka shafi kasashen sun a tsohon tarihi.

Da alamu batun kisan gilla gad an jarida Jamal Kashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul bai shafi ziyarar ba, ko kuma a ce ziyarar ta dinke rashin jituwa tsakanin Saudiyya da Turkiyya kan wannan akasin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.