A ruwan wuta da Israila ta yi kan Gaza na tsawon kwana 11 da zummar murkushe ‘yan Hamas, yara ne su ka fi galabaita da shiga firgici inda har a ka kashe fiye da yara 60 a ruwan boma-bomai da amfani da jiragen yaki 160.
An rusa dubban gidaje da ruguza harkokin kasuwanci da katse hanyoyin samun ruwan sha ga mutum 800,000.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar Palasdinawa 248, rushe kimanin gidaje da wajajen kasuwanci 17,000, ruguza makarantu 53, ruguza asibitoci 6, ruguza masallatai 4 da lalata kashi 50% na hanyoyin ruwan sha.
Asarar dukiya da Palasdinawa su ka yi ta kai darajar dala miliyan 150.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀