• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAR SANATA GOJE TA YI MURABUS DAGA GWAMNATIN INUWA YAHAYA

‘Yar tsohon gwamnan jihar Gombe Hussaina Goje ta yi murabus daga gwamnatin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe.

Hussaina dai ta kasance kwamishina ta ma’aikatar muhalli da gandun daji a karkashin gwamnatin ta APC da ta hau gado a 2019.

Hussaina ta baiyana dalilan kashin kai su ka saka ta daukar matakin murabus din inda ta godewa gwamnan don dama da ya ba ta na aiki a matsayin ‘yar majalisar zartarwar jihar.

Masu sharhi na ganin murabus din bai rasa nasaba da rashin fahintar juna tsakanin gwamna Inuwa Yahaya da mahaifin na ta.

A ranar jumma’a tawagar tsohon gwamnan ta gamu da turjiya wajen shigowa gari inda matasa su ka nemi fito na fito da juna.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.