• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANZU NA ZAMA MARAYA A SIYASA BIYO BAYAN RASUWAR BALARABE MUSA-ABDULKARIM DAIYABU

Shugaban rundunar adalci Alhaji Abdulkarim Daiyabu ya ce rasuwar tsohon gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya sa ya zama maraya don dama shi daya ya saura ma sa a tafiyar siyasar Najeriya.

Daiyabu wanda ke zantawa da manema labaru a ofshin sa da ke Nassarawa GRA Kano, ya ce samun mai akidar kaunar talakawa irin na Balarabe sai an tona kuma dama shi ne kadai ya ke ganin mai sauran akida a tsakanin ‘yan siyasa.

Abdulkarim Daiyabu wanda ya koyi lamuran siyasa daga Mallam Aminu Kano, Chief Obafemi Awolowo da Mallam Inuwa Dutse, ya yi fatar wasu matasan ‘yan siyasa za su taso don maye gurbin marigayan don amfana akasarin al’ummar Najeriya da ya ke talakawa ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
60 thoughts on “YANZU NA ZAMA MARAYA A SIYASA BIYO BAYAN RASUWAR BALARABE MUSA-ABDULKARIM DAIYABU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.