• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANZU HAKA AN SAKO KARIN MUTUM BIYAR CIKIN FIYE DA MUTUM 30 DA A KA SACE A AFAKA, KADUNA

A daidai lokacin rubuta wannan labarin an sako mutum 5 cikin fiye da 30 da a ka sace a makarantar kimiyyar gandun daji ta Afaka da ke jihar Kaduna.

Tun farko an samu nasarar sako mutum biyar inda yanzu ya nuna an samu sako mutum 10 kenan.

Wadanda a ka sako yanzu da ke kan hanyar komawa gida sun hada da mata 4 da namiji daya.

Da ya ke magana ta wayar tarho daya daga wadanda a ka sako mai suna Abdulganiyu Aminu ya ce su na mawuyacin hakin yunwa don rashin ingancin abincin da a ke ba su.

Hakanan ya kara da cewa an tattara kudin fansa  a ka biya kafin sako su kuma a kan zabi wadanda su ka fi galabaita ne a sako.

Aminu ya bukaci gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai ya bi matakan tattaunawa don sako sauran wadanda ke hannun miyagun irin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *