• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANZU AIKI YA SAMU HUKUMAR ZABE WAJEN TSARA JADAWALIN ZABEN 2022-AISHA JIBIR DUKKU

Shugabar kwamitin zabe ta majalisar wakilan Najeriya Aisha Jibir Dukku ta ce aiki ya samu hukumar zaben Najeriya INEC don aikin tsara jadawalin zaben 2023.
Aisha Dukku na magana ne jim kadan bayan sanya hannu kan sabuwar dokar zabe da shugaba Buhari ya yi a fadar Aso Rock.
Dukku ta ce dama rashin sanya hannu kan dokar ce ya sa jinkiri fito da jadawalin zaben kama daga na ‘yan majalisa, gwamnoni zuwa shugaban kasa.
‘Yar majalisar ta kara da cewa za su koma majalisa su baje a faifai bukatar da shugaba Buhari ya yi na a duba sashe na 84 na dokar, ta na mai cewa babban abun farin ciki an samu sanya hannu kan dokar kamar yanda ya yi alkawari kuma ta fara aiki nan take.
Hakanan ta ce ko da gabanin zaben 2023 a ka samu damar gudanar da wani zabe, to da dokar za a yi amfani.
An samu labarin hukumar zaben, za ta yi zama a asabar din nan don duba dokar da fara tsara jadawalin babban zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YANZU AIKI YA SAMU HUKUMAR ZABE WAJEN TSARA JADAWALIN ZABEN 2022-AISHA JIBIR DUKKU”
  1. Hi there! I just would like to give you a big thumbs up for the great information you
    have here on this post. I’ll be coming back to your blog for more
    soon.

Leave a Reply

Your email address will not be published.