• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANKIN PALASDINAWA YA AUKA DA JUYAYIN BAYAN ISRAILA TA BINDIGE ‘YAR JARIDA SHIREEN ABU AKLEH

Yankin Palasdinawa ya auka cikin matukar juyayi biyo bayan bindige shahararriyar ‘yar jarida Bapalasdiniya Shireen Abu Akleh da sojojin Isra’ila su ka yi.

Sojojin na Isra’ila sun harbi Shireeen Abu Akleh a ka a daidai sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin.

Da farko Isra’ila ta so shashatar da kisan da nuna harsashi ne da ya yi batan kai daga Palasdinawan wajen musayar wuta ya kashe ta. Daga bisani babban hafsan sojan kasar Laftanar Janar Aviv Kochavi ya dawo daga batun da nuna ba tabbas na yanda ‘yar jaridar ta mutu kuma Isra’ila ta yi nadamar aukuwar hakan.

Amurka ta nuan takaicin kisan Shireen da zaiyana kisan da murkushe ‘yancin ‘yan jarida.

Shireen Abu Akleh ta shahara a labarum da ta kan bayar kan ukubar da Palasdinawa ke sha a hannun Isra’ila.

Hatta editan marigayiyar wato Ali Samoudi ya samu rauni bayan harbin sa da a ka yi a gadon baya amma ya na samun sauki a asibiti.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.