• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANKIN LEKKI A LAGOS YA ZAMA SABUWAR TUNGAR ‘YAN DAMFARAR YANAR GIZO-EFCC

ByYusuf Yau

Sep 4, 2021 , , ,

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta aiyana yankin Lekki a Lagos da cewa ya zama sabuwar tungar masu damfarar yanar gizo.

Yankin Lekki na mallakar mutane masu samun kudin shiga daidai gwargwado da sauran ‘yan boko.

EFCC a sanarwar da ta fitar ta ce a tsakanin watan Afrilu da Yuni kadai sun cafke mutum 403 da ke alaka da damfarar yanar gizo.

Hukumar ta ce wannan ya nuna yankin na Lekki ya zama mafakar ‘yan damfarar ta aiki da na’ura mai kwakwalwa.

Yawancin wadanda a ka kama matasa ne da ke tsakanin shekaru 25-34.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YANKIN LEKKI A LAGOS YA ZAMA SABUWAR TUNGAR ‘YAN DAMFARAR YANAR GIZO-EFCC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.