• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YANKEWAR MAN FETUR YA HADDASA DOGAYEN LAYUKAN NEMAN MAI A ABUJA

ByNoblen

Dec 8, 2021 ,

Yankewar kawo man fetur ya haddasa dogayen layukan masu neman man fetur a gidajen fetur a babban birnin Najeriya Abuja.
Yayin da ma’abota motoci ke bin dogon layi, matasa masu sayar da man a jarka sun baiyana rike da tiyo su na sayarwa masu gajin hakuri kan farashi mai tsada.
A lokacin da lamarin ya yi tsanani har ya kai ga wasu gidajen man sun rufe inda wasu ‘yan baranda ke amsar na goro su na shigar wasu ta barauniyar hanya.
Zuwa rubuta wannan labari lamarin ya yi sauki bayan mutane sun cika tankunan su don gudun ko-ta-kwana.
Akalla wasu masu mota kan cika tanki su koma gefe su juyewa ‘yan bakar kasuwa su sake dawowa don cika tankunan.
Duk hakan na faruwa gabanin sanarwar kara farashin litar man.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *