• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TAWAYEN HOUTHI SUN DANDANA KUDAR SU A YANKIN MARIB

ByNoblen

Jun 24, 2021 , ,

‘Yan tawayen houthi a Yaman da Iran ke marawa baya sun dandana kudar su hannun sojojin gwamnati a yakin kwatar birni mai tasiri na arewacin kasar, Marib.

Majiyoyin gwamnatin kasar ta Abed Rabbo sun ce a kwana biyu da su ke wuce, dakarun gwamnati su  hallaka mayakan houthi da daman gaske.

‘Yan tawayen houthi sun samu akasin ne a mummunan hari da su ke kai garin Al-Mashjah da Al-Kasara da ke yankin na Marib.

A sanadiyyar fadan ‘yan houthi 63 ne su ka rasa ran su inda magoya bayan gwamnati 27 su ma su ka riga mu gidan gaskiya.

Jami’in sojan gwamnati Laftanar Kanar Rashad Al-Mekhlafi ya ce yakin ya tagaiyara ‘yan tawayen houthi inda su ka rasa dubban mayaka ciki har da kwamandoji.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
61 thoughts on “‘YAN TAWAYEN HOUTHI SUN DANDANA KUDAR SU A YANKIN MARIB”

Leave a Reply

Your email address will not be published.