• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TALIBAN A AFGHANISTAN SUN KWACE BIRNI NA UKU MAFI GIRMA “HERAT”

‘Yan Taliban a Afghanistan su na kara nausawa don kifar da gwamnatin kasar a birnin Kabul.

Yanzu haka Taliban ta kwace Herat wanda shi ne birni na uku mafi girma a kasar.

Tu. gabanin nan Taliban ta kwace garin Ghazni da ke tsakanin Kabul da Kandahar.

Kungiyar Taliban ta shiga Kandahar wanda a baya nan ne kashin bayan ta, inda ta sake wadanda ke gidan yari da su ka hada da mayakan ta.

Da alamu tun janyewar Amurka daga Afghanistan bayan zama na shekaru 20, ‘yan Taliban ke cin galaba kan sojojin gwamnati.

Zai yi wuya gwamnatin Kabul ta kai labari duk da tayin raba madafun Iko da Taliban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *