• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TAKARAR SHUGABANCIN APC SUN KARA DAGEWA DA KAMFEN A ABUJA

‘Yan takarar neman shugabancin jam’iyyar gwamnati APC sun kara dagewa da kamfen musamman a babban birnin Najeriya Abuja ta hanyar baza hotuna da rubutun manufofin su in sun samu nasara.
Hakanan ‘yan takarar kan yi amfani da yanar gizo ko shiga kafafen labaru masu zaman kan su don yayata muradin na su da nuna sun fi juna dacewa da hawa kujerar.
Akasarin masu son takarar tsoffin gwamnoni ne da su ka kammala wa’adin mulki karo biyu har ma wasu daga cikin su yanzu haka ‘yan majalisar dattawa ne.
Za a gudanar da zaben a lokacin babban taron jam’iyyar a ranar 26 ga watan nan a dandalin taruka na Abuja “eagle square”
Daga yanda a ke ganin wadanda su ka fito takarar na nuna daga yankin arewa ne, sai dai ba wani sashe a siyasance da a ka ware ma sa kujerar tsakanin sassan siyasar yankin 3.
Ba za a yi mamaki ba in shugaban jam’iyyar ya fito daga arewa, jam’iyyar ta tura tikitin takarar shugaban kasa a inuwar ta ga kudanci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN TAKARAR SHUGABANCIN APC SUN KARA DAGEWA DA KAMFEN A ABUJA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.