• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TAKARAR SHUGABAN KASA A MANYAN JAM’IYYU NA RANGADIN NEMAN GOYON BAYA

‘Yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyu na cigaba da takarkarewa ga zaga jihohin da musamman su ke da yawan wakilai don neman goyon baya a zaben fidda gwani.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki kalilan gabanin manyan tarukan jam’iyyun a karshen watan nan don fidda ‘yan takarar.

A jam’iyyar APC mai mulki a taraiya da ke da kimanin ‘yan takara 30, a na ganin ‘yan takarar da su ka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da uban jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu na zaga jihohin arewa maso da su ka fi yawan kuri’u.

Jigon APC Ibrahim Masari da ke mara baya ga Tinubu na cewa Osinbajo ba zai taka mu su birkin samun kai wa ga gaci ba duk da kasancewar sa a fadar Aso Rock.

PDP da ke adawa na yunkurin saita kan ‘yan takarar ta da su ka hada da gwamnoni, manyan jami’an gwamnati da su ka yi fice da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gefe guda.

Magoya baya Atiku na nuna shi kadai zai iya yi wa APC zarra a zaben yayin da wasu ke cewa ya dace a gwada wani sabon dan takara.

Gwamna Bala Muhammad na Bauchi na cikin gwamnonin da ke takarar, ya na mai cewa su na da hikimar dawo da Najeriya kan turbar arziki.

Sauran jam’iyyun adawa na nuna za su iya ja da manyan guda biyu matukar jama’a su k adage don kawo sabon canji.

Manjo Hamza Almustapha da ya tsaya a jam’iyyar AA na cewa alamun jam’iyyar kadai sun isa nuna kyakkyawar alkibla.

Koma me za a ce, hukumar zabe na jiran sunayen ‘yan takara zuwa 3 ga watan gobe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “‘YAN TAKARAR SHUGABAN KASA A MANYAN JAM’IYYU NA RANGADIN NEMAN GOYON BAYA”
 1. Hello There. I found your weblog the use of msn. That
  is a very smartly written article. I will
  be sure to bookmark it and come back to read extra of your
  useful info. Thanks for the post. I’ll definitely comeback.

 2. Nice post. I was checking continuously this weblog and I’m inspired!
  Extremely useful info particularly the closing section 🙂 I
  care for such information much. I was looking for this certain info for a
  long time. Thanks and best of luck.

 3. Whats up very nice website!! Man .. Excellent .. Amazing .. I’ll bookmark your blog and take the feeds additionallyKI’m satisfied to seek out a lot of helpful information here in the put up, we need work out extra techniques on this regard, thank you for sharing. . . . . .

Leave a Reply

Your email address will not be published.