• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TAKARA DA YAWA SUN SHA MAMAKI A ZABEN FIDDA GWANI

‘Yan takarar tikitin jam’iyyar PDP na majalisa sun sha mamaki don yanda zaben bai fito bisa tunanin su ba.
Abun mamakin ya faru ne ga ‘yan takarar da ke ganin kan su, su na da tagomashi amma su ka wayi gari wasu ‘yan takarar da ba a yi tsammani ba su ka lashe zaben.
Duk da PDP ta samu koma baya a wasu manyan jihohi na rashin tsayaiyun ‘yan takara, amma an samu sabbin fuskoki a cikin ‘yan takarar majalisa.
Za a zuba ido a ga yanda zaben fidda gwani na gwamnoni a inuwar jam’iyyar zai gudana ko shi ma zai ba da mamaki a jihohin da jam’iyyar ba ta ga gwamna.
Masana na cewa yawan ‘yan takarar ya haddasa shan mamakin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “‘YAN TAKARA DA YAWA SUN SHA MAMAKI A ZABEN FIDDA GWANI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.