• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TA’ADDAN BOKO HARAM SUN KAI HARI A KAUYEN KATARKO DA KE JIHAR YOBE

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 24, 2021

‘Yan ta’addan da ba tababar ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan kauyen Katarko da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Rahoton da jaridar PREMIUN TIMES ta wallafa ya baiyana cewa miyagun sun shiga garin ne a motoci 10 da tunkarar cibiyar soja da ke garin.

Harin ya sa mutanen kauyen arcewa zuwa duhuwar daji don tsira da ran su.

Da alamun yanda labarin ya nuna ‘yan ta’addan sun yi awun gaba da wasu makamai daga cibiyar bayan musayar wuta.

Garin ya saba samun harin miyagun irin da kan haddasa asarar rayuka da dukiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN TA’ADDAN BOKO HARAM SUN KAI HARI A KAUYEN KATARKO DA KE JIHAR YOBE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.