• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN TA’ADDA SUN SHIGA RANN DA KE KALABALGE A BORNO

‘Yan ta’addan DAESH a Afurka da hadin guiwar Boko Haram sun shiga garin Rann da ke karamar hukumar Kalabalge a jihar Borno.

Rahaotanni sun nuna miyagun sun shigo garin na kan iyakar Najeriya da Kamaru su na bude wuta.

Hakanan ya sa jama’ar gari su ka arce don samun mafaka a dazuka.

Wannan hari na zuwa ne daidai lokacin da a ke samun ‘yan ta’addan na ajiye makamai su na mika wuya ga gwamnati.

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya ce ‘yan ta’addan 3000 su ka mika wuta ga Najeriya inda 900 su ka yi saranda a Kamaru.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN TA’ADDA SUN SHIGA RANN DA KE KALABALGE A BORNO”
  1. Howdy! This article couldn’t be written any better! Going through
    this article reminds me of my previous roommate! He constantly kept preaching
    about this. I’ll send this post to him. Pretty sure he’s going to have a
    good read. Many thanks for sharing!

Leave a Reply

Your email address will not be published.