• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN SIYASA NA FADAR DALILAN DA SU KE GANIN GWANAYEN SU NE ZA SU LASHE ZABE

ByNasiru Adamu El-hikaya

Jun 16, 2022

Magoya bayan manyan ‘yan siyasa na fadar dalilan da su ke ganin ganin gwanayen su ne za su lashe babban zaben 2023.

Muhawarar ta fi daukar hankali a babbar jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa.

Yayin da APC ta tsaida tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takara. PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takara.

A 2007 Atiku ne dan takarar shugaban kasa na tsohuwar jam’iyyar Tinubu wato ACN wacce ta narke da sauran manyan jam’iyyu ta zama APC ta zamanin yau.

‘Yan APC na cewa Tinubu zai samu kuri’un yarbawa a cure inda zai hada da wadanda zai samu daga gwamnonin APC na arewa da ke mara ma sa baya.

Magoya bayan Atiku na cewa zai samu dimbin kuri’u daga ‘yab arewa da su ka gaji da salon mulkin Buhari inda zai samu na wanda zai tsayar a matsayin mataimaki daga kudu.

Hakanan wasu na nuna Atiku ya fi Tinubu koshin lafiya don haka masu son sauya shugaba da zai zama kullum ya na kan hanyar asibitocin turai zai zabi Atiku.

Duk da haka a na ganin manyan masu ruwa da tsakin siyasa da ke cikin gwamnati za su dage don Tinubu ya samu mulki don su ma hakan ya ba su damar makalewa a madafun iko.

Wani dalilin da a ke ganin zai taimaki Atiku shi ne yankin arewa maso gabar inda ya fito da bai taba samar da shugaba ba; amma Tinubu na iya samun ta sa nasarar ta hanyar masu ganin ai bayan dan arewa ya yi shekaru 8 kan mulki ya dace mulkin ya koma kudu ba tare da la’akari da kowace jam’iyya ba.

In an bi ta yawan dangi Atiku zai iya cin gajiyar kusaci ga Huasa Fulani da hakika sun fi yarbawa yawa amma zafin marawa kabialnci baya ya fi tsanani a tsakanin yarbawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.