• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN SANDA SUN SHIGA FARAUTAR MASU KISAN GILLA A KUDU MASO GABASHIN NAJERIYA

Rahoto ya tabbatar da cewa ‘yan sanda na daukar matakan farautar masy kisan gilla don kabilanci a yankin kudu maso gabar.

Masu kai hare-haren ‘yan awaren IPOB kan yi amfani da manyan bindigogi su na harbe ‘yan arewa da ke ysnkin da kuma jami’an tsaro.

Shaharerren dan sanda DCP Abba Kyari na jagorantar wata tawagar kwararrun jami’ai da ke farautar masu kisan gillar.

Labari ya nuna samamen ‘yan sandan ya rutsa da daya daga kwamandojin ‘yan IPOB mai taken Dragon.

Zuwa yanzu za a ce gwamnati na bin lamarin a hankali wajen murkushe masu kisan gillar don kar gagarumin hsri ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ko kuma akasin hukunta wanda ba shi da laifi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.