• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN SANDA SUN SAKO SURUKIN ROCHAS OKOROCHA WATO UCHE NWOSU

ByNoblen

Dec 28, 2021

Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun sako surukin tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha wato Uche Nwosu.
Tun farko wasu ‘yan sanda sun shigo cikin majami’ar da Nwosu ke taron godiya bayan bison mahaifiyar sa, su ka yi awun gaba da shi.
Nwosu dai da alamun ya sha wuya a hannun jami’an da a ka ba da labarin sun mare da ma yaga ma sa riga.
An ga wani hoto da ke nuna Nwosu daure da ankwa amma ba a nuna sauran mutanen da ke tare da shi ba ko ma bayanin dalilin kama shi da sanya ma sa ankwar.
Tuni masu raderadi ke dangantaka cafke Nwosu da tsama ko gaba da ke tsakanin gwamnan jihar Hope Uzodinma da Rochas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YAN SANDA SUN SAKO SURUKIN ROCHAS OKOROCHA WATO UCHE NWOSU”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *