‘Yan sanda a birnin Istanbul na Turkiyya sun kama mutum 17 bayan shirya zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da nada shugaban jami’a da ba sa marawa baya.
Daruruwan dalibai su ka shirya zanga-zangar a Istanbul bayan shugaba Raceb Tayyeb Erdoan ya aiyana nada Melih Bulu a matsayin shugaban jami’ar Bogazici.
Melih Bulu dai ya taba tsayawa neman shugabancin jam’iyyar shugaba Erdoan a 2015.
Zanga-zangar na rashin amincewar jama’a kan kutsowar ‘yan siyasa a lamuran ilimin kasar.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀