• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN SANDA 3 SUN RASA RAN SU A HATSARIN MOTAR ‘YAN SANDA A ABUJA

An samu hatsarin motar ‘yan sanda a Abuja inda jami’an ‘yan sanda uku su ka rasa ran su nan take yayin da sauran wadanda ke motar su ka samu munanan raunuka.
Hatsarin ya auku ne sanadiyyar fashewar taya yayin da motar ke gudun kure taya kan hanyar Kubwa zuwa Zuba.
Rahoton ya baiyana cewa a lokacin da tayar ta fashe motar ta bar kan titi ta auka magudanar ruwa daura da anguwar Gwarinpa inda jami’an su ka rasa rai.
Majiyar ta nuna ‘yan sandan na aikin rakiya ne a wani aiki na musamman da zai kai su Kaduna.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Abuja Josephine Adeh ta tabbatar da aukuwar hatsarin da nuna juyayin abun da ya faru.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *