• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN SA KAI A SOKOTO SUN HALLAKA MUTUM 11 CIKI HAR DA LIMAMI

 

‘Yan sa kUai ko a ce ‘yan banga sun kashe mutum 11 ciki da wani limami a kauyen Mamanda da ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto.

Nan take dai wadanda ‘yan sa kan su ka kai wa hari su ka riga mu gidan gaskiya inda 4 daga ciki da su ka samu raunuka a ka kai su asibiti.

Da alamu kisan ya auku ne don limamin da sauran wadanda a ka kashe Fulani ne da a ke samun dangin su na daji na aikata miyagun laifuka.

Lamarin ‘yan banga tun farko ya zama tamkar ramuwar gaiya ne na kabilanci da ke neman raba kan Hausawa da Fulani a yankin arewa maso yamma.

Limamin dai na jan sallah ne a daya daga masallatan salloli 5 a garin Salame da ke nan karamar hukumar ta Gwadabawa.

Wadanda a ka kasha sun fito ne daga matsugunan Fulani a yankin kuma sun zo kasuwar ne ta Mamande don sayan kayan abinci yayin da ‘yan bangar su ka kashe su.

Rahoton ya nuna ‘yan Sa kan sun fito ne daga karamar hukumar Goronyo inda su ka farwa Fulanin da su ke zargin na alaka da barayin daji.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya haramta aikin ‘yan sa kan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “YAN SA KAI A SOKOTO SUN HALLAKA MUTUM 11 CIKI HAR DA LIMAMI”
  1. Spot on with this write-up, I seriously think this
    amazing site needs a lot more attention. I’ll probably be back again to read through more, thanks for the advice!

  2. Hello! This is my first visit to your blog! We are
    a group of volunteers and starting a new project in a community
    in the same niche. Your blog provided us useful information to work on. You have done a marvellous job!

Leave a Reply

Your email address will not be published.