• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN NAJERIYA SUN FARA NUNA DAMUWA GA YIWUWAR KARA FARASHIN LITAR FETUR

ByNoblen

Mar 28, 2021

Al’ummar Najeriya sun fara nuna damuwa ga alamun da ke nuna geamnati za ta kara farashin man fetir da adadin kudi mai yawa.

Wannan ya biyo bayan yanda shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyaru Kolo ke cewa gwamnati na biyan tallafi duk wata da ya kai har Naira biliyan 120 duk wata don litar mai ta zauna kan Naira 162.

NNPC dai na nuna geamnati ba za ta cigaba da jure biyan tallafin ba, don asalin kudin da litar ke tashi a yanzu N234.

A yanar gizo dai mutane na nuna bacin ran ne da nazarin yanda kayan masarufi za sy yu tsada matukar a ka kara farashin.

Duk da haka akwai wasu da ke fatar samun kudin saya duk tsadar litar.

A Najeriya ko jita-jita a ka yada cewa za a kara farashin man, mutane kan garzaya gudajeb mai don cika tankunan su don cin gajiyar mai sauki kafin fara shan mai tsada.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *