• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN NAJERIYA SUN DAGE SAI DA SU KA GA BAYAN RUNDUNAR YAKI DA ‘YAN FASHI TA ‘YAN SANDA “SARS”

ByNoblen

Oct 11, 2020 , , ,

Gabanin soke rundunar yaki da ‘yan fashi da babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu ya sanar, ‘yan Najeriya a jihohi da dama sun dage da kamfen din neman lalle rundunar ‘yan sanda ta soke sashen na ta mai yaki da ‘yan fashi “SARS” don samun su da cin zarafin al’umma, wuce gona da iri dama kashe wasu ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba, kuma kan tuhumar da ba a kammala bincike ba.

Duk da sanarwar da tun farko babban sufeton ya fitar da ke baiyana dakatar da sintirin ‘yan SARS da takaita aikin su ga yaki da ‘yan fashi; hakan sam bai gamsar da jama’a ba da ke son a soke su gaba daya, har haka ta cimma ruwa.

Hatta mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya nuna bacin rai ga aiyukan na ‘yan SARS bayan kashe wani matashi a Lagos inda ya gana da babban sufeto da umurtar sa ya yi garambawul ga rundunar don ta dace da tsarin kare hakkin ‘yan adam.

A baya an sha yin garambawul ga rundunar,amma ba wani sauyi da a kan gani sai ma sabon salon muzgunawa jama’a.
Ofishin ‘yan sandan SARS na Abuja a cike ya ke kullum makil motoci tamkar tashar mota na mutanen da a ka kama ko kuma masu zuwa don neman belin ‘yan uwan su.
Yanzu dai babban sufeton ya ce za a bullo da tsarin yaki da ‘yan fashi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN NAJERIYA SUN DAGE SAI DA SU KA GA BAYAN RUNDUNAR YAKI DA ‘YAN FASHI TA ‘YAN SANDA “SARS””
  1. Spot on with this write-up, I absolutely believe that this amazing site needs far more
    attention. I’ll probably be returning to see more, thanks for
    the info!

Leave a Reply

Your email address will not be published.