• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

‘YAN NAJERIYA NA CIKIN DAMUWAR SHIRIN KARA FARASHIN LITAR FETUR

ByNoblen

Dec 29, 2021

Yayin da a ke haramar shiga sabuwar shekara ta 2022, ‘yan Najeriya na nuna matukar damuwa kan shirin gwamnatin na janye dukkan tallafin man fetur da hakan zai sa lita ta kai Naira 320-340 daga Naira 162.
A halin da a ke ciki dai, ba da tallafin fetur zai zama ba ya kan doka zuwa watan fabreru don haka komai zai iya faruwa na dan karen tsada.
A ‘yan kwanakin nan a nan Abuja a kan wayi gari a ka matasa sun fito da jarakuna kan titi su na sayar da fetur a bakar kasuwa inda wasu gidajen man kan rufe amma daga bisani ko can dare sai lamari ya koma daidai.
Duk da ma’aikatan gidajen mai kan ce rashin isowar tankunan dakon mai ne don rufe wata muhimmiyar hanyar da su ke bi, mutane sun shiga fargabar hakan shiri ne kamar yanda a ka saba in za a kara farashin fetur.
Shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyari Kolo ya baiyana cewa duk wata gwamnati kan kashe tsakanin Naira biliyan 100-120 kan tallafi amma yanzu ba za ta iya cigaba da kashe makudan kudin ba, za ta goge tsarain a kundin ta.
Talakawa da ‘yan hamaiya na caccakar gwamnatin ta APC da ta sha alkawarin daidaita lamura har ma da alwashin da shugaba Buhari ya yi tun kamfen na gugar zanar bai dace lita ta yi tsada ba.
Halima Kajuru ‘yar hamaiya ce da ke cewa duk alkawuran da a ka dauka ba a gani a kasa ba.
Masana da masu hannu a lamuran fetrur sun sha ba da shawarar kafa knanan matatun fetur din da hakan zai sa a rika tace man da a ke bukata daga cikin gida.
Koma dai me za a ce tuni farashin kayan masarufi ya yi tashin gauron zabi, ballantana a ce litar fetur ta cilla, ba shakka kuncin zai kai kure taya.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “‘YAN NAJERIYA NA CIKIN DAMUWAR SHIRIN KARA FARASHIN LITAR FETUR”
  1. Its like you read my mind! You appear to know a lot about this, like you wrote the book in it or something.
    I think that you could do with some pics to drive the message home
    a little bit, but instead of that, this is excellent blog.

    A fantastic read. I will definitely be back.

  2. I was very happy to search out this web-site.I wished to thanks for your time for this glorious learn!! I positively having fun with every little little bit of it and I have you bookmarked to check out new stuff you weblog post.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *