• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN MAROKO SUN YI BAN-KWANA TA KARSHE GA RAYAN AWRAM-YARON DA YA RASU BAYAN FADAWA RIJIYA

ByNoblen

Feb 8, 2022

Daruruwan mutane a Maroko sun taru makabartar kauyen Ighran don ban-kwana ga yaron nan Rayan Awram wanda ya rasa ran sa sanadiyyar fadawa rijiya mai zurfi.
Rayan dai ya fada rijiyar mai zurfin kafa 100 ranar talata inda sai ranar asabar a ka samu dauko shi bayan tona wani rami a gefen tsauni har a ka isa bigiren da ya ke kwance a kasan rijiyar.
Mutane sun jira sa’ao’I da dama don jiran jana’izar da yin juyayi mai yawan gaske.
Hatsarin da ya rutsa da yaron mai shekaru 5 kacal ya dauki hankalin duniya inda a ka yi ta fatar a samu fito da shi da rai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
56 thoughts on “‘YAN MAROKO SUN YI BAN-KWANA TA KARSHE GA RAYAN AWRAM-YARON DA YA RASU BAYAN FADAWA RIJIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.