• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

‘YAN MAJALISA 9 NA PDP A KANO SUN BI JAM’IYYAR KWANKWASO

‘Yan majalisar jiha a Kano karkashin inuwar PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ta tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kakakin majalisar dokokin Kano Uba Abdullahi ya gabatar da sanarwar ‘yan majalisar ta sauya sheka.
‘Yan majalisar sun baiyana dalilin rashin hadin kai a reshen jam’iyyar na Kano da ma taraiya a matsayin dalilin sun a ficewa daga cikin ta.
A na sa ran ‘yan siyasar adawa da dama da ma watakila wasu daga APC za su koma NNPP don hadewa da Kwankwaso gabanin zaben 2023.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *