• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN ISWAP/BOKO HARAM SUN KAI HARI A JIHAR YOBE

ByYusuf Yau

Sep 27, 2021

‘Yan ta’addan ISWAP/Boko Haram sun kai hari kan babban birnin karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe inda su ka yi musayar wuta da jami’an tsaron Najeriya.
Babban birnin mai suna Babangida na tazarar kilomita 50 a kudu maso gabar daga babban birnin jihar Damaturu.
Rahoton ya baiyana cewa an yi musayar wuta tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan ta’addan da ke luguden wuta da bindigogin su don su samu cin Karen sub a babbaka a garin.
Ba mamaki mummunan barin wuta da yawan ‘yan ta’addan, ya sa nan take a ka tura Karin dakaru don karfafa guiwar wajen da su ke dauki ba dadi da b’yan ta’addan.
Lamarin Boko Haram da ya fara tun 2009 na sauya kamannin salon hare-hare don yanda muradu da lokaci ke sauyawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *