• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN HOUTHI SUN YI BIRIS DA SHIRIN ZAMAN LAFIYA NA KUNGIYAR LARABAWA

‘Yan tawayen houthi a Yaman sun yi biris da shirin zaman lafiya da kungiyar kasashen larabawa ta yi tayin jagoranta a birnin Riyadh.
Houthi wacce Iran ke marawa baya ta ki amincewa da shirin da zai iya kawo karshen yakin basasar Yaman da ya faro tun 2014.
Tun farko an tsara taron zai fara daga ranar 29 ga watan nan zuwa 7 ga watan gobe.
Maimakon haka houthi na cigaba da rike babban birnin kasar San’a’a da bukatar rundunar larabawa ta dawo da zababbiyar gwamnati a Yaman ta daina daukar matakan hana ta walwala a San’a’a da kuma tsahar teku ta Hodeida.
Gwamnatin Yaman mai helkwata a birni n Aden na kudanci na baiyana cewa ta san houthi za ta ki amincewa da tayin salamar in an duba tarihin yanda ta yi biris da irin wannan tsari a baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “‘YAN HOUTHI SUN YI BIRIS DA SHIRIN ZAMAN LAFIYA NA KUNGIYAR LARABAWA”
  1. It?¦s really a nice and useful piece of information. I?¦m glad that you simply shared this helpful information with us. Please keep us informed like this. Thank you for sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published.