• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN HOUTHI SUN SACE ‘YAN GUDUN HIJIRA DAGA AFURKA FIYE DA 220

ByNoblen

Apr 4, 2021

Rahoto na baiyana cewa kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya ta sace fiye da ‘yan gudun hijira daga Afurka 220 a kasar da fitina ta yi wa illa.

Houthi sun sace ‘yan gudun hijirar ne a ‘yan sa’o’i da su ka wuce daga wajajen da majalisar dinkin duniya ke kula da su a birnin Sanaa.

Bayanai sun nuna 55 daga wadanda ‘yan tawayen su ka sace mata ne.

Tun fako ‘yan gudun hijirar sun yi zanga-zangar neman a bincika yanda ‘yan houthi su ka yi sanadiyyar tashin gobara a daya daga sansanonin ‘yan gudun hijira inda fiye da ‘ysn Afurka 40 su ka kone kurmus.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *