• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN HOUTHI SUN KASHE KWAMANDAN SOJAN GWAMNATIN YAMAN JANAR NASSER AL-THAYBANI

ByNoblen

Dec 14, 2021 ,

‘Yan tawayen Yaman mabiya shi’a da Iran ke turawa makamai da goyon baya, sun kashe kwamandan sojan gwamnatin Yaman Janar Nasser Al-Thaybani a wajen birnin Marib.
Marigayin na jagorantar sojoji don kare yankin tsaunuka na Al-Balaq da ke kallon birnin Marib wanda ‘yan houthi ke yi wa barin wuta.
Janar Nasser wanda ya yi nasarar tura ‘yan tawayen baya, ya yi numfashin san a karshe bayan wani gwanin harbi dan houthi ya auna kokon kan sa ya harba ma sa albarushi.
Hare-haren rundunar hadin guiwar larabawa sun rutsa da kimanin ‘yan houthi 100 da su ka yi wo farmakin bazata a Balaq.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN HOUTHI SUN KASHE KWAMANDAN SOJAN GWAMNATIN YAMAN JANAR NASSER AL-THAYBANI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *