• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN HAMAIYA A ISRAILA SUN YI TARON DANGI DON KAWAR DA NETANYAHU DAGA KUJERA

Masu adawa da firaministan Israila da ya fi dadewa kan mulki Benjamin Netanyahu sun hada gangamin kawar da shi daga kujera.

Masu adawar sun zabi Naftali Bennet da ke kan gaba a adawar ya zama sabon furaminista.

Shugaban adawar kasar Yair Lapid ya ba da sabarwar taron dangin kuma tuni sun sanarwa shugaban kasar wannan muradi.

Tsarin dai ta nuna Bennett zai yi mulki na shekaru biyu inda Yair Lapid zai cikata wa’adin sauran shekaru biyu.

Yarjejeniyar cikin dare ta dakatar tafiya zabe a karo na biyar cikin kimanin shekaru biyu don dambarwar da kan haddasa haka.

Karamar jam’iyyar Larabawa musulmi na cikin wannan yarjeniya a karo na farko a tarihin siyasar kasar ta Yahudawa.

A makon gobe majalisar dokokin kasar KNESSET za ta kada kuri’a kan wannan yarjejeniya da hakan zai kawo karshen mulkin Netanyahu.

A na sa bangare, Netanyahu zai yi duk abu mai yiwuwa wajen hana nasarar wannan kuri’a don samun makalewa kan madafun iko.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.