• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN FANSHO ZA SU SHIGA YAJIN CIN ABINCI DON RASHIN BIYAN SU KUDIN AJIYE AIKI

‘Yan fansho a jihar Anambra, Najeriya sun yi barazanar shiga yajin cin abinci don nuna takaici kan rashin biyan su kudin ajiye aiki run shekaru hudu da su ka wuce.

Shugaban kungiyar ‘yan fansho na jihar Anthony Ugozor ya baiyana korafin a wata sanarwa a babban birnin jihar Awka.

Wannan dai don matsa lamba ga gwamnan jihar Willie Obiano ne ya biya su kudin ajiye aikin.

Anthony ya ce a taron da za su yi mako mai zuwa za su dau mataya kan shiga yajin cin abinci duk da hakan ka iya zama barazana ga lafiyar su in an duba yawan shekarun su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.