• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BOKO SUN KI TAIMAKAWA CIGABAN NAJERIYA-SHUGABA BUHARI

ByNoblen

Sep 15, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aza alhakin rashin samun cigaban da a ke bukata a Najeriya kan ‘yan boko da ya ce sun ki tunanin da zai taimakawa kasar.

Shugaban na magana ne a jihar Imo bisa gaiyatar gwamnan jihar Hope Uzodinma don bude wasu aiyuka da gwamnan ya kammala aikin su.

Shugaban ya ce daga 1999 da farar hula su ka shigo zuwa 2015 Najeriya na samun makudan kudi inda gangar fetur kan kai dala 100 kuma a kan hako ganga miliyan biyu da rabi a duk wuni.

Shugaba Buhari ya kara da cewa duk kokarin da gwamnatin sa ke yi wajen samar da cigaban kasa na samun cikas don kalubalen tsaro.

Wannan ba shi ne karo na farko da shugaban ke dora alhakin samun koma baya a Najeriya ga gwamnatocin da su ka gabaci gwamnatin sa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “‘YAN BOKO SUN KI TAIMAKAWA CIGABAN NAJERIYA-SHUGABA BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.