• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BOKO HARAM SUN KAI FARMAKI KAN CIBIYAR SOJA A KAMARU SU KA KASHE SOJOJI 7

‘Yan ta’addan boko haram sun kai hari kan wata cibiyar soja a Kamaru inda sojoji 7 ciki da kwamandan su, su ka rasa ran su.

Akasin ya auku ne a Segme da ke kuryar arewacin Kamaru.

Wannan shi ne mafi munin hari da a ka samu asarar rayuka daga hare-haren boko haram a arewacin Kamaru.

Ba a samu adadin wadanda su ka mutu a bangaren ‘yan ta’addan ba kuma sun zo ne a motoci 6.

‘Yan boko haram kan tashi daga yankin jihar Borno a Najeriya su shiga yankin Kamaru.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *