• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN YI KISAN GILLA GA MUTUM 5 A YANKIN BAKURA A JIHAR ZAMFARA

‘Yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Rogoji da ke yankin karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara inda su ka yi kisan gilla ga mutum 5.
Labarin ya baiyana cewa ‘yan bindigar sun shiga garin ne don huce haushin ga yanda mutane su ka samar da bayanai ga jami’an tsaro da ‘yan sintiri kan ‘yan bindigar.
Hakan ya nuna abun da kan biyo bayan kokarin jama’a na fallasa ‘yan ta’addan don maganin su daga hukumomin tsaro.
Miyagun irin sun zabi daidai lokacin sallar asuba su ka kai harin kuma duk da jajircewar ‘yan banga bai hana ta’annatin ‘yan bindigar ba.
Majiya ta baiyana cewa kwazon ‘yan bangar ya takaita barnar ‘yan bindigar da su ka so daidaita kauyen gaba daya.
Don fargabar yiwuwar dawowar ‘yan bindigar, mutane sun fice daga kauyen.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “‘YAN BINDIGA SUN YI KISAN GILLA GA MUTUM 5 A YANKIN BAKURA A JIHAR ZAMFARA”
  1. Wow! After all I got a weblog from where I be able to in fact take valuable facts concerning my study and knowledge.

Leave a Reply

Your email address will not be published.