• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN SHIGA KAUYUKAN ANKA A JIHAR ZAMFARA

ByNoblen

Jan 6, 2022 ,

Rahotanni daga jihar Zamfara na baiyana cewa ‘yan bindiga sun shiga kauyukan karamar hukumar Anka inda su ka firgita jama’a.
Wani mazaunin yankin da ya sha da kyar, ya baiyana cewa ‘yan bindigar sun kai mutum 500 kuma su kan taho ne kan babura.
Yanzu dai cewar mutumin da ya bukaci a boye sunan sa, mutanen kauyuka fiye da 5 sun bazama zuwa cikin garin Anka inda su ka samu mafaka.
Mutumin ya nuna babbar hanyar waraka ko samun saukin lamarin shi ne mutane su taya su da addu’a don hakan shi ne mafita ba ya ga aikin jami’an tsaro.
Hatta a wannan harin a na raderadin da hannun madugun ‘yan bindiga Bello Turji wanda ya turo wasikar neman sulhu ga masarautar Shinkafi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *