• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN SHIGA KARAMAR HUKUMAR BUNDUGU HAR SU KA YI WA WANI BASARAKE KISAN GILLA

ByNoblen

Dec 31, 2021 , ,

‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun shiga kauyen Gada a yankin karamar hukumar Bungudu inda su ka yi kisan gilla ga sarkin garin mai suna Umaru Bawan-Allah.
Rahoton ya baiyana cewa ‘yan bindigar sun auka garin ne da sanyin safiyar laraba inda su ka yi kisan gilla ga basaraken da wasu mutum uku.
‘Yan bindigar sun yi mugun aikin na su tsawon sa’a 4 su na kisan gilla har ma da banka wuta kan motoci da kayan abinci a fadar sarkin.
In za a tuna hatta shi kan sa sarkin Bungudu Hassan Attahiru ya taba fadawa hannun ‘yan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda su ka rike shi fiye da wata daya kafin su sake shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN SHIGA KARAMAR HUKUMAR BUNDUGU HAR SU KA YI WA WANI BASARAKE KISAN GILLA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *