• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN SAKE YARA UKU DA SU KA KAMA DA SAURAN MUTANE A MARU

ByNoblen

Nov 15, 2021

‘Yan bindiga a yankin Maru da ke jihar Zamfara sun sako yara uku da su ka sace da sauran mutane wajen wata hudu da su ka wuce.
Rahoton ya nuna ‘yan bindigar sun sako yaran ba tare da karbar kudin fansa ba biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin su da manoma a yankin.
A kan samu wasu yankuna da ‘yan bindiga ke shafawa wasu sassa lafiya don kulla wata yarjeniya.
Wannan na nuna zuwa yanzu gagarumin matakan da a ke dauka da zummar murkushe barayin bai gama kai wa ga gaci ba.
Baya ga babban birnin jihar Zamfara Gusau, sassan jihar na cikin yanayin datsewar sadarwar salula don samun damar kofar rago ga barayin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN SAKE YARA UKU DA SU KA KAMA DA SAURAN MUTANE A MARU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.