• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN KASHE ‘YAN SANDA BIYU A ANAMBRA

‘Yan bindiga sun kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a jihar Anambra inda su ka kashe ‘yan sanda biyu.

Tun farko miyagun irin sun kai kona ofishin ‘yan sandan a yankin Obosi da ke karamar hukumar Idemili ta arewa, kafin su kashe ‘yan sandan.

Tuni rundunar ‘yan sandan a jihar ta tura jami’an ta don binciken yanda lamarin ya faru da yunkurin cafke ‘yan bindigar.

Tuni a ka adana gawawwakin ‘yan sandan biyu a dakin ajiye gawa da ke kusa da inda akasin ya auku.

Irin wadannan hare-hare sun fara zama ruwan dare a kudu maso gabar da kudu maso yammacin Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *