‘Yan bindiga da ke cin karen su babbaka a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi kisan gilla ga shugaban matasan jam’iyyar APGA a yankin Nnewi ta kudu Mr.Emeka Alaehobi.
‘Yan bindigar sun sace Mr.Alaehobi ranar alhamis inda sai dai a ka tsinci gawar sa a yashe.
Kashe-kashe da kan faru a yaakin sun faro ne daga batun kafa kasar ‘yan aware ta Biyafara inda ‘yan bindigar kungiyar awaren IPON/ESN ke bindige mutanen da bas a kauna ko musamman ‘yan arewacin Najeriya da ke kananan sana’o’I a yankin.
Rundunar ‘yan sanda a jihar ta baiyana tura jami’an ta don cafko wadanda su ka yi kisan don fuskantar hukunci.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀