• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN KASHE KWAMISHINAN FANSHO NA KOGI ADEBAYO SOLOMON

Rahotanni na baiyana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta kan motar da ke dauke da kwamishinan fansho na jihar Kogi Adebayo Solomon inda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran sa.

Solomon na tafiya ne daga Ilorin babban birnin jihar Kwara zuwa wani garin Kabba a jihar Kogi inda akasin ya auku.

An ruwaito kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi Ayuba Ede na cewa tuni an kaddamar da bincike kan lamarin.

An kai gawar Solomon wani asibiti a garin Egbe da ke jihar Kogi.

Duk wannan na nuna yanda lamuran tsaro su ka tabarbare a sassan Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *