• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN KAI HARI KAN WATA MAJAMI’A A JIHAR ONDO

Rahotanni daga jihar Ondo na baiyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan wata majami’a a jihar inda hakan ya yi sanadiyyar asarar rayuka.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce ‘yan bindiga sun kawo farmakin ne yayin da mahalarta majami’ar ke ibadar ranar lahadi.

Baya ga wadanda su ka rasa ran su an samu wasu ma da su ka samu raunuka.

Masu sharhi na nuna irin hakan bait aba faruwa a baya ba a jihar don haka ya firgita mutane.

Rundunar ‘yan sandan ta dau matakan dawo da salama a yankin da lamarin ya faru da kuma baza jami’ai don kamo wadanda su ka kai harin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN KAI HARI KAN WATA MAJAMI’A A JIHAR ONDO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.