• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN KAI HARI KAN GIDAN YARIN KABBA A JIHAR KOGI

‘Yan bindiga sun kai hari kan gidan yarin garin KABBA da ke jihar Kogi a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Miyagun irin sun kashe jami’an gidan yarin biyu da kuma sako fursunoni da dama.

A yayin harin, jami’an soja 15, ‘yan sanda 10 da jami’an gadin gidan yarin 10 sun yi dauki ba dadi da ‘yan bindigar amma cikin juyayi soja daya da dan sanda daya sun rasa ran su, yayin da kuma zuwa yanzu ba a ga jami’an gidan yarin biyu ba.

An shaidawa ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola akasin da a ka samu.

Ba wata kungiya da ta hau alhakin kai wannan farmaki.

Wannan ba shi ne karo na farko da a ke samun kai hari a gidan yari a sassan Najeriya da kunce fursunoni ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.